KOWA YA BAR GIDA ...

KOWA YA BAR GIDA ...

Dandalin Nishadantarwa, Ilmantarwa da Fadakarwa

Dandalin Nishadantarwa, Ilmantarwa da Fadakarwa


BARKA DA ZUWA WANNAN SHAFI NA KOWA YA BAR GIDA...!

Wannan Shafi ne da aka kirkireshi musamman domin Bunkasa da kuma zakulo kyawawan al'adun Hausawa wadanda aka fara mantawa dasu kodai don cigaban zamani da muke cikinsa wanda yayi sanadiyyar da yawa daga cikin Matasa basu damu da wadannan kyawawan dabi'u da al'adu ba, ko kuma saboda rikon sakainar kashi da suke yiwa wannan Harshe mai cike da hikimomi da kuma al'adu masu ban kayi.
Bugu da kari, wayewar zamani ta sanya da yawa daga cikin mutane masu ikirarin su Hausawa ne sunyi kasa a guiwa wajen koyar da Yaran masu tasowa tsagwaron Yarensu na ainihi wanda har ta kai ga zaka samu matashi ba zai iya magana ta dakika ashirin ba tare da ya sanyo wata kalma ta Turanci ba. Ko shakka babu irin wannan lamari yayi kamari ta yadda ya sanya hatta lamirai sukan sha wahala a Hannun wasu daga cikin matasa, inda zaka samu wani ya dauki lamirin namiji ya bawa mace, ko lamirin mace ya bawa namiji.
Irin wannan rashin kulawa na daga cikin abubuwan da suka kai wasu yarukan suka dushashe ko kuma suka gurbata, har aka samu damar shigar masu da wasu kalmomi suka maye gurbin kalmomin su na ainihi; Duk mai lura zai ga cewa shima Harshen/Yaren Hausa yana fuskantar irin wannan kalu-bale. Misali guda da zamu bayan anan shine kalmar (OKAY), wannan kalmar zaka samu da yawa daga cikin Hausawa har ma wadanda basu yi boko ba tayi tasiri a harasansu.
Duba da wadannan dalilai da wasu da bamu samu damar ambatarsu ba anan muka ga dacewar samar wa 'yan Uwa Hausawa da wannan shafin na KOWA YA BAR GIDA... inda zamu rika kawo ma mabiya wannan shafin namu KARIN MAGANA, SALON MAGANA, WASA KWAKWALWA, AL'ADU da dai sauransu.
Zaku kuma iya tallata Hajojinku a wannan shafin namu a cikin farashi mai sauki.

© Hakkin Mallaka, Kowa Ya Bar Gida... 2019 - 2020