KOWA YA BAR GIDA ...

KOWA YA BAR GIDA ...

Dandalin Nishadantarwa, Ilmantarwa da Fadakarwa

Dandalin Nishadantarwa, Ilmantarwa da Fadakarwa


YARUKAN NA'URA MAI KWAKWALWA A HARSHEN HAUSA

YARUKAN NA'URA MAI KWAKWALWA A HARSHEN HAUSA

Kimiyya da Fasaha abubuwa ne da Zamani yake tattare dasu wanda kowanne Zamani da abinda yake kawowa, amma da yawa daga cikin mutane basa amfani da damar da suke da ita wajen cin gajiyar fasaha da kimiyya da zamaninsu ya zo dasu. Fasahar/Yarukan Na'ura mai kwakwalwa (PROGRAMMING LANGUAGES) abubuwa ne da wannan zamani yake dauke dasu, wanda kafin wannan lokaci babu wani abu mai kama da wannan.
Duk da cewa wannan fasaha da samu shekaru da ba zasu kasa talatin ba a baya Al'ummar mu ta Hausawa basu rungumi wannan fasaha a matsayin abinda zasu amfana dashi ba idan aka kwatanta da wasu kabilu a wannan kasar tamu. Wata kila wannan ana da nasaba da rashin wadatuwar wadanda zasu koyar damu a cikin Yarenmu na Hausa ta yadda zamu fahimci abin kamar yadda ya dace. Ba mamaki don ba'a samu wanda zai karantar da wannan fasaha ba a cikin Harshen Hausa kasancewar fasaha ce da kusan duk wanda zai koye ta zai koyeta ne da yaren Turanci kuma juya ta a kuma karantar da ita da wani harshe wanda ba Turanci ba abu ne mai wahala. Amma wannan bai hana wasu su karantar da ita a cikin yarensu, kamar Indiyawa da wasu daga cikin yarukan yankin Gabas ko kuma yakin (Asia), Haka ma Larabawa ba'a barsu a baya ba wajen karantar da wannan fasahar a yarensu ba.
Saboda haka -duk da cewa- zai yi wahala a fassara dukkanin kalmomin da ake amfani dasu a wannan Yarukan zuwa wani yaren da ba turanci ba, muma zamu yi iya kokorinmu wajen kawo ma mai koyo abinda idan har ya bishi sau da kafa zai fahimci kaso mai tsoka (70%) a cikin (100%) na wannan fasahar.
Amma muna son mu sanar daku cewa bamu yi alkawarin kawo maku dukkan bayanan a cikin harshen Hausa ba. Saboda haka yana da kyau mai sha'awar koyon wannan fasahar ya dauka cewa wannan ba zai wadatar dashi ba idan har yana son ya kware sosai a cikin wannan fasahar.
Bayan kammala kowanne Yaren a cikin yarukan da zamu koyar daku a wannan shafin, muna sa ran zaku iya neman abinci da wannan fasahar gwargwadon abinda mai koyo ya samu ya kuma fahimta.© Hakkin Mallaka, Kowa Ya Bar Gida... 2019 - 2021